-
Ma'aikatan Gwamnati Na Yajin Aikin Kwana 10 A Guinea Bissau
Jul 25, 2018 06:35A Guinea Bissau ma'aikata sun tsunduma wani yajin aiki na kwanaki goma, domin cilasta wa gawmnati yi masu karin albashi da kuma inganta yanayin aikinsu.
-
Shugaban China Ya Isa Kasar Rwanda
Jul 23, 2018 07:39Shugaban kasar China Xi Jinping ya fara ziyarar aiki a kasar Ruwanda
-
Ana Shirin Ayyana Karshen Ebola A DR Congo
Jul 23, 2018 02:44A wani lokaci nan da mako guda ne ake sa ran hukumomi a jamhuriya Demokuradiyyar Congo, zasu sanar da kawo karshen cutar Ebola a yankin Equator dake arewacin kasar.
-
Boko Haram Ta kashe Mutum 18 A Chadi
Jul 23, 2018 02:42Wasu mayaka da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun kashe mutane 18 da kuma yin awan gaba da mata 10, a lardin Dabua na Chadi dake yankin tafkin Chadi.
-
Shugaban Kasar China Ya Fara Gudanar Da Ziyarar Aiki A Nahiyar Afrika
Jul 21, 2018 07:48Shugaban kasar China ya fara gudanar da ziyarar aiki a nahiyar Afrika, inda a halin yanzu haka ya isa kasar Senegal.
-
Ran Gadin Ministar Tsaron Faransa A Yankin Sahel
Jul 21, 2018 01:17A ci gaba da ran gadin da take a yankin Sahel domin karfafa wa kungiyar G5 Sahel, kan yaki da mayakan dake ikirari da sunan jihadi, ministar tsaron kasar Faransa, Florence Parly, ta isa a birnin Ouagadugu na kasar Burkina Faso.
-
Ministar Tsaron Faransa Na Ziyara Nijar Don Karfafa Wa Kungiyar G5 Sahel
Jul 20, 2018 06:13Ministar tsaron kasar Faransa, Florence Parly, ta fara wata ziyarar aiki a Jamhuriya Nijar, domin karfafa wa kungiyar yaki da ta'addanci ta G5 Sahel.
-
MDD Ta Damu Da Ruruwar Rikicin Tsakiyar Mali
Jul 19, 2018 01:15Babban kwamishinan hukumar kare hakkin bil adama ta Majalsiar Dinkin Duniya, ya nuna matukar damuwarsa akan yadda rikicin kabilanci ke kara kamari a tsakiyar kasar Mali.
-
Ivory Coast : Ouatara Ba Zai Yi Takara A 2020 Ba
Jul 17, 2018 01:22Shugaba Alhassan Ouatara na Ivory Coast, ya ce ba zai tsaya takara ba a zaben shugabacin kasar dake tafe na 2020.
-
Najeriya : Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum 44 A Katsina
Jul 17, 2018 01:21Rahotanni daga Najeriya na cewa, mutane 44 ne suka rasa rayukansu kana wasu 20 na daban suka bata sakamakon ambaliyar ruwan sama da aka samu a kashen makon jiya a jihar Katsina dake arewa maso yammacin kasar.