Najeriya : Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum 44 A Katsina
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32356-najeriya_ambaliyar_ruwa_ta_kashe_mutum_44_a_katsina
Rahotanni daga Najeriya na cewa, mutane 44 ne suka rasa rayukansu kana wasu 20 na daban suka bata sakamakon ambaliyar ruwan sama da aka samu a kashen makon jiya a jihar Katsina dake arewa maso yammacin kasar.
(last modified 2018-08-22T07:02:07+00:00 )
Jul 17, 2018 01:21 UTC
  • Najeriya : Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum 44 A Katsina

Rahotanni daga Najeriya na cewa, mutane 44 ne suka rasa rayukansu kana wasu 20 na daban suka bata sakamakon ambaliyar ruwan sama da aka samu a kashen makon jiya a jihar Katsina dake arewa maso yammacin kasar.

Gwamnan jihar Aminu Belllo Masari, ya shaidawa manema labarai jiya cewa, sama da gidaje 500 ne suka lalace a yankin karamar hukumar Jibiya dake jihar.

Aminu Masari, ya ce gwamnati ta tsugunar da wadanda iftila'in ya shafa a wata makarantar firamare dake yankin.

A cewarsa, ya sanar da gwamnatin tarayyar kasar game da iftila'in, ya na mai jadadda cewa tuni hukumar bada agajin gaggawa ta kai manyan motoci 13 shake da kayakin jin kai da za a raba ga mutanen, da wannan iftila'in da ba a taba gani ba a jihar Katsina da ma wasu sassan kasar ya shafa.