Ivory Coast : Ouatara Ba Zai Yi Takara A 2020 Ba
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32357-ivory_coast_ouatara_ba_zai_yi_takara_a_2020_ba
Shugaba Alhassan Ouatara na Ivory Coast, ya ce ba zai tsaya takara ba a zaben shugabacin kasar dake tafe na 2020.
(last modified 2018-08-22T07:02:07+00:00 )
Jul 17, 2018 01:22 UTC
  • Ivory Coast : Ouatara Ba Zai Yi Takara A 2020 Ba

Shugaba Alhassan Ouatara na Ivory Coast, ya ce ba zai tsaya takara ba a zaben shugabacin kasar dake tafe na 2020.

Mista Ouatara ya bayyana hakan ne a yayin kafa wani sabon kawancen jam'iyyu siyasa a kasar mai suna (RHDP), da ya kunshi jam'iyyu masu mulki, in banda jam'iiyar PDCI, ta Henri Konan Bedie.

Shugaban kasar mai ci ne ya karbi jagorancin wannan sabon kawancen siyasa, inda kuma a cikin jawabinsa ya fayyace manufofin siyasar kawacen a zaben 2020.

A cikin jawabin nasa Mista Ouatara, ya ce, ''Yau Faransa na da shugaba dan shekara 40, wanda ba wai yana nufin na tsufa ba, amma hakan sako ne na tunani'' duniya na canzawa, zamuyi aiki kafada da kafada da shugaba Bedie domin mika mulki ga sabbin tasowa a shekara 2020.

Jam'iyar PDCI ta Henri Konan Bedie, wacce ta goyi bayan shugaba Ouatara a zaben shugabancin kasar har sau biyu, bata yarde shiga wannan sabon kawancen na RHDP ba, saboda kin gamsuwa da tayin da aka mata.