Shugaban China Ya Isa Kasar Rwanda
Shugaban kasar China Xi Jinping ya fara ziyarar aiki a kasar Ruwanda
Wannan ziyara dai ita ce karo na fara da wani shugaban kasar China ya kai a nahiyar Afirka , inda bayan da ya fara da kasar Senegal ya wuce zuwa birnin Kigali na Kasar Rwanda inda ake sa ran nan gaba ,shugabanin biyu za su gabatar da taron maema labarai a wannan talata, sannan a ranar Laraba, ya wuce zuwa Afirka ta Kudu domin halartar taron kasashen duniya masu samun habakar tattalin arziki wato Brics a birnin Johanneshurg.
Ziyarar Xi dai na zuwa ne a daidai lokacin da Chinan ke fuskantar gagarumar hamayya a fannin kasuwanci daga gwamnatin Shugaba Donald Trump na Amirka, wanda gwamnatinsa ba ta damu sosai da kulla alaka da nahiyar ta Afirka ba, yankin da ke zaman na biyu mafi yawan al'umma a duniya.