MDD Ta Damu Da Ruruwar Rikicin Tsakiyar Mali
Babban kwamishinan hukumar kare hakkin bil adama ta Majalsiar Dinkin Duniya, ya nuna matukar damuwarsa akan yadda rikicin kabilanci ke kara kamari a tsakiyar kasar Mali.
Da yake bayyana hakan a wani taron manema labarai a birnin Geneva, kakakin hukumar ta HCDH, Rupert Colville, ya ce abun damuwa ne halin da ake ciki a jihar Mopti dake tsakiyar kasar ta Mali, inda rikicin ya kai ga tsallake iyakokin da aka shata wa bangarorin dake rikicin.
A baya bayan dai, kwararu kan kare hakkin bil adawa dake cikin tawagar MDD a Malin, sun gano cewa fararen hula da dama a yankunan da rikicin ya shafa na kaurace wa muhallansu saboda ruruwar rikicin.
Tun farkon wannan shekara bayanan da hukumar ta fitar sun nuna cewa an samu rikicin kabilaci 99, galibi a jihar ta Mopti wadanda suka janyo hasarar rayukan fararen hula a kalla 289.
Rikicin dai ya shafi 'yan kabilar Dogon da Bambara wadanda galibi manoma ne da kuma Fulani makiyaya.