-
An Kaddamar Da Gidauniyar Tallafa Wa Ilimin Yara A Dakar
Feb 03, 2018 02:56Shugaba Emanuel Macron na Faransa ya kaddamar da wata gidauniyar kasa da kasa ta tallafa wa tsarin bada ilimi ga yara musamman a Afrika a brinin Dakar na kasar Senegal.
-
Libiya : Bakin Haure 10 Suka Suka Mutu A Teku
Feb 03, 2018 02:56Rahotanni daga Libiya na cewa bakin haure a kalla goma ne suka gamu da ajalinsu a yayin da kwale-kwalen dake dauke dasu ya nutse a teku akan hanyarsu ta zuwa Turai.
-
An Sake Kashe Sojojin Kamaru A Arewa Maso Yamma
Feb 01, 2018 13:46An kashe wasu jami'an tsaro Jandarma biyu na Jamhuriya Kamaru a yankin masu magana da turancin ingilishi a arewa maso yammacin kasar.
-
Libiya : An Hana 'Yan Yankin Da Ya Goyi Bayan Ghaddafi Komawa Gida
Feb 01, 2018 13:20A Libiya dubban iyalai ne na birnin Tawarga da suka bar yankin bayan hambarar da mulkin tsohon shugaban kasar, Mua'mmar Ghaddafi, aka hana su komawa gida, kamar yadda wata yarjejeniya da suka cimma da gwamnatin hadin kan kasar ta tanada.
-
Mutum 950 Sun Makale A Karkashin Kasa A Afrika Ta Kudu
Feb 01, 2018 12:52Rahotanni daga Afrika ta kudu na cewa masu aikin hakar zinari 950 ne suka makale a karkashin kasa, sakamakon wata guguwa data janyo daukewar wutar lantarki a lardin Free State dake tsakiyar kasar.
-
Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci A Kyautata Rayuwar Mutanen Afrika
Jan 30, 2018 08:44Babban sakataren Majalisar dinkin duniya António Guterres ya yi kira ga shuwagabannin kasashen Afrika da su kyautata rayuwar mutanen kasashensu don hana su shiga gudun hijira ba bisa ka'ida ba.
-
Laberiya : Weah, Zai Rage Albashinsa Da Kashi 25%
Jan 30, 2018 02:53Sabon shugaban kasar Laberiya, George Weah, ya sanar da anniyarsa ta rage albashinsa da wasu kudade da yake samu da kashi 25 cikin dari, saboda matsin tattalin arziki da kasar ke fama da shi.
-
Amurka Ta Nemi Kasashen Afrika Da Su Yanke Alakar Jakadanci Da Koriya Ta Arewa
Jan 29, 2018 15:20Kasar Amurka ta sanya matsin lamba kan kasashen nahiyar Afrika domin su yanke alakar jakadanci da kasar Koriya ta Arewa.
-
Manyan 'Yan Siyasar Masar Sun Yi Kira Da A Kaurace Wa Zaben Shugaban Kasar
Jan 29, 2018 02:23Wasu gungun 'yan siyasa da masu fadi a ji a kasar Masar sun bukaci al'ummar kasar da su kaurace wa zaben shugaban kasar da za a gudanar a watan Maris mai kamawa saboda abin da suka kira danniya da ake nunawa sauran 'yan takara da nufin share fagen yin tazarcen shugaba Abdel Fattah al-Sisi na kasar.
-
An Sake Kashe Sojojin Mali Hudu
Jan 28, 2018 14:40Majiyoyi daga Mali na cewa an sake kashe wasu sojojin kasar hudu a arewa maso gabashin kasar a iyaka da Jamhuriya Nijar.