An Kaddamar Da Gidauniyar Tallafa Wa Ilimin Yara A Dakar
Shugaba Emanuel Macron na Faransa ya kaddamar da wata gidauniyar kasa da kasa ta tallafa wa tsarin bada ilimi ga yara musamman a Afrika a brinin Dakar na kasar Senegal.
An dai kaddamar da shirin ne tare da halartar wasu shuwagabannin kasashen Afrika da suka hada da Nijar, Mali, Burkina faso baya ga Senegal da ta yi hadin gwiwa da faransa wajen shirya taron, da kuma wakilai na manyan masu zuba jari.
Dukkan bangarorin sun sha alwashin matsa kaimi don tallafa wa tsarin bada ilimi ga yara, musamman 'ya 'ya mata wadanda a koda yaushe suke ke cikin ha'u'la'i a cewar shugaba Macron.
Biritaniya ce dai sahun gaba wajen zuba kudaden raya tsarin, inda ta alkawarta bada dala miliyan 417, sai kungiyar EU dala miliyan 400 da Norway dala 260 a yayin da Faransa ta kara kan alkawarin data yi zuwa Dala miliyan 250.
Jakadiyar tsarin, tauraruwar duniya Rihanna wacce ta halarci taron na Dakar ta yaba da ci gaban da tsarin ya samu, tana mai cewa ba zasu fasa kokawa ba kan batun, har sai ko wanne yaro da yarinya ya samu ilimi.
Sai dai shugabar asusun kula da yara na MDD, Unicef, Henrietta Fore ta bukaci a kara zage dantse don suna bukatar linkin dala Bilyan 3,1 da aka samu kawo yanzu.