Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci A Kyautata Rayuwar Mutanen Afrika
(last modified Tue, 30 Jan 2018 12:14:18 GMT )
Jan 30, 2018 12:14 UTC
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci A Kyautata Rayuwar Mutanen Afrika

Babban sakataren Majalisar dinkin duniya António Guterres ya yi kira ga shuwagabannin kasashen Afrika da su kyautata rayuwar mutanen kasashensu don hana su shiga gudun hijira ba bisa ka'ida ba.

Majiyar muryar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta nakalto António Guterres yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a taron shuwagabannin Afrika karo na 30 a birnin Addis Ababa na kasar Habasha. 

Babban sakataren ya kara da cewa yin hijira zuwa kasashen da suka ci gaba a wani lokaci yana da amfani don yana bunkasa tattalin arzikin kasashen kuma yana rage rashin dai-daito tsakanin al-umma. Amma duk da haka ya kirayi shuwagabannin kasashen na Afrika su samar da yanayi a kasashensu wanda zai hana matasa ficewa zuwa wasu kasashen don neman aiki.