Laberiya : Weah, Zai Rage Albashinsa Da Kashi 25%
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27759-laberiya_weah_zai_rage_albashinsa_da_kashi_25
Sabon shugaban kasar Laberiya, George Weah, ya sanar da anniyarsa ta rage albashinsa da wasu kudade da yake samu da kashi 25 cikin dari, saboda matsin tattalin arziki da kasar ke fama da shi.
(last modified 2018-08-22T07:01:21+00:00 )
Jan 30, 2018 02:53 UTC
  • Laberiya : Weah, Zai Rage Albashinsa Da Kashi 25%

Sabon shugaban kasar Laberiya, George Weah, ya sanar da anniyarsa ta rage albashinsa da wasu kudade da yake samu da kashi 25 cikin dari, saboda matsin tattalin arziki da kasar ke fama da shi.

Mista Weah wanda ya ce zai aiwatar da hakan ba tare da wata wata ba, ya kuma yi kira ga 'yan majalisar datijjan kasar da suyi koyi da hakan.

Bayanai sun nuna cewa albashin da tsohuwar shugabar kasar, Ellen Johnson Sirleaf, ke dauka ya kai Dalar Amurka 90,000 a shekara.

A wani jawabinsa gaban 'yan majalisar dattijan kasar, Weah, ya kuma sanar da cewa zai gabatar da wani shiri na aiwatar da kwaskwarima ga wata ayar doka ta kundin tsarin mulkin kasar dake nuna wariyar launin fata, da kuma inganta harkokin ilimi.

Ya kuma kalubalanci wani matakin kasar na hana 'yan kasashen waje mallakar filaye da kuma samun takardar zama dan kasa, wanda a cewarsa ya hana wasu haifafun 'yan kasar mallakar takardar zama dan kasa bayan yakin kasar da ya tilasta masu hijira a tsakanin (1989-2003).