Mutum 950 Sun Makale A Karkashin Kasa A Afrika Ta Kudu
Rahotanni daga Afrika ta kudu na cewa masu aikin hakar zinari 950 ne suka makale a karkashin kasa, sakamakon wata guguwa data janyo daukewar wutar lantarki a lardin Free State dake tsakiyar kasar.
Kakakin kamfanin hakar zinarin na Sibanye-Stillwater ya shaidawa tashar talabijin ta eNCA cewa, ba'a samu fitar da ma'aikatan da sukayi aiki a cikin daren jiya ba daga cikin mahakar, sakamakon daukewar wutar lantarki da aka samu.
Saidai ya ce an fiddo wasu 64 daga cikin ma'aikatan da suka makale a mahakar mai zurfin mita dubu guda.
Amma kamfanin ya ce dukkan ma'aikatan da alamu suna cikin kofin lafiya, kuma ana kan aike masu abinci da ruwan sha.
A nata bangare kungiyar masu aikin hako ma'adinai ta (AMCU) ta koka da abunda ta kira sakaci, saboda kamfanin bai yi tananin wasu dabaru na samar da wutar lantarki ba idan irin wannan mugun hadari ya faru.
Irin wannan hadari, ba sabon abu ne ba a Afrika ta Kudu, kasa mafi yawan wuraren hakar ma'adinai masu zurfi a duniya, inda a shekara 2015, mutum 77 ne suka gamu da ajalinsu a cikin irin wannan aiki.