An Sake Kashe Sojojin Mali Hudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27725-an_sake_kashe_sojojin_mali_hudu
Majiyoyi daga Mali na cewa an sake kashe wasu sojojin kasar hudu a arewa maso gabashin kasar a iyaka da Jamhuriya Nijar.
(last modified 2018-08-22T07:01:21+00:00 )
Jan 28, 2018 14:40 UTC
  • An Sake Kashe Sojojin Mali Hudu

Majiyoyi daga Mali na cewa an sake kashe wasu sojojin kasar hudu a arewa maso gabashin kasar a iyaka da Jamhuriya Nijar.

Wata majiyar soji da tabbatar da labarin ta ce maharan sun isa wurin ne kan babura da kuma motoci, kafin daga bisani su harba makamin roka a sansanin sojojin kasar.

Bayanai daga kasar sun ce jiragen faransa masu saukar ungulu na shawagi kan yankin a safiyar yau Lahadi.

Ko a ranar Asabar ma sojojin kasar 14 ne suka ne suka gamu da ajalisu kana wasu 18 suka raunana a wani hari da 'yan ta'adda suka kai a sansanin Sumpi dake nisan kilomita kimanin dari da kudu maso yamma na birnin birnin Tumbuktu.