-
Shugaban Kasar Rasha Ya Yi Furuci Da Cewa: Amurka Tana Taimakon 'Yan Ta'adda A Kasar Siriya
Dec 15, 2017 12:19Shugaban kasar Rasha ya yi furuci da cewa: Sojojin Amurka suna taimakawa 'yan ta'addan kasa da kasa da aka jibge a cikin kasar Siriya domin kada a murkushe su.
-
Amurka Da Saudiyya Sun Taimakawa (IS) Mallakar Muggan Makamai_ Rahoton (CAR)
Dec 15, 2017 05:15Kungiyar (CAR) dake sa ido kan yadda ake amfani da makaman yaki da kayan soji na kasa da kasa, ta fitar da wani rahoto, wanda ke cewa makaman yakin da kasashen Amurka da Saudiyya suka mikawa 'yan tawaye a Siriya ya taimakawa 'yan ta'adda IS sosai.
-
Iran Ta Yi Watsi Da Zargin Mikawa 'Yan Houtsi Makami Mai Linzami
Dec 15, 2017 04:29Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta yi watsi kwata kwata da zarge-zarge marar tushe da jakadiyar Amurka a MDD, Nikki Haley, ta yi, na cewa makami mai linzamin da 'yan gwagwarmayar neman sauyi na Houtsi a Yemen suka harba zuwa birnin Riyad na kasar Saudiyya, kirar Iran ne.
-
John Kerry: Ficewar Amurka Daga Yarjejeniyar Kare Muhalli Abin Kunya Ne.
Dec 12, 2017 18:52Tsohon sakataren harkokin wajen kasar ta Amurka ya soki matakin da Shugaban kasarsa Donald Trump ya dauka na ficewa daga yarjejeniyar kare muhalli ta duniya.
-
Qudus : Matakin Trump, Ayyana Karshen Isra'ila Ne _ Nasrallah
Dec 11, 2017 16:08Shugaban Kungiyar Hezbollah ta kasar Labanon, Sayyid Hassan Nasrallah, ya bayyana cewa matakin Trump na Amurka kan ayyana Qudus babban birnin yahudawan sahayoniya 'yan mamaya shelanta kawo karshen Isra'ila ne.
-
Amurka : An Kai Hare-haren Bam A birnin New York
Dec 11, 2017 15:31'Yan sanda a birnin New York na Amurka sun ce mutum hudu ne suka raunana sakamakon fashewa wasu abubuwa a tashar jirgin kasa ta Times Square dake yankin Manhattan.
-
Shugaban Kasar Venezuala Ya Bayyana Shirin Kasarsa Na Kalubalantar Duk Wani Makircin Kasar Amurka
Dec 10, 2017 19:02Shugaban kasar Venezuala ya jaddada cewa: Al'ummar Venezuala suna cikin shirin kalubalantar duk wani makircin kasar Amurka musamman matakin wuce gona da iri kan kasarsu.
-
Bayanin Bayan Taron Kasashen Larabawa Akan Kudus
Dec 10, 2017 07:34Da safiyar yau lahadi ne kasashen taron gaggawa na ministocin harkokin wajen kasashen larabawa ya fitar da bayani da ya kunshi yin tir da matakin shugaban kasar Amurka akan birnin kudus
-
Matsayin Qudus : Kwamitin Tsaro Na MDD Ya Juyawa Amurka Baya
Dec 09, 2017 05:54Kwamitin tsaro na MDD ya maida Amurka saniyar ware dangane da matakin shugaba Donald Trump na ayyana Qudus a matsayin babban birnin yahudawan sahayoniya 'yan mamaya na Isra'ila.
-
Matsayin Qudus : Limamin Al-Azhar Ya Soke Ganawarsa Da Mataimakin Trump
Dec 09, 2017 05:53Babban limamin jami'ar Al-Azhar na kasar Masar, Ahmed al-Tayeb, ya soke ganawarsa da mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence, a matstayin maida martani kan matakin Trump na ayyana Qudus babban birnin Isra'ila.