Amurka : An Kai Hare-haren Bam A birnin New York
'Yan sanda a birnin New York na Amurka sun ce mutum hudu ne suka raunana sakamakon fashewa wasu abubuwa a tashar jirgin kasa ta Times Square dake yankin Manhattan.
Shugaban 'yan sanda yankin James O'Neill ya shaidawa masu aiko da rahotanni cewa wani matashin ne dan shekaru 27 ya yi kai harin mai nasaba da na ta'addanci, kuma an yi nasara cafke shi.
An dai bayyana matashin da ya yi jigida da wani abun fashewa da sunan Akayed Ullah wanda dan asalin kasar Uzbekistan ne da cewa ya yi mubayi'a ga kungiyar 'yan ta'adda ta IS.
Wasu rahotanni daga kasar sun ce shi ma matashin ya ji rauni sakamakon harin.
Wannan harin dai na zuwa ne a kasa da makwanni biyu da wani harin babbar mota da ya hallaka mutum takwas da kuma raunana wasu 12 a kudancin yankin na Manhattan, wanda shi ne na farko tun bayan harin 11 ga watan Satumban 2001 a birnin New York.