John Kerry: Ficewar Amurka Daga Yarjejeniyar Kare Muhalli Abin Kunya Ne.
Tsohon sakataren harkokin wajen kasar ta Amurka ya soki matakin da Shugaban kasarsa Donald Trump ya dauka na ficewa daga yarjejeniyar kare muhalli ta duniya.
Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato tsohon sakataren harkokin wajen na kasar Amruka wanda yake halartar taron kare muhalli a birnin Paris na Faransa yana cewa; Fitar da Amurka daga cikin yarjejeniyar ta kare muhalli da Trump ya yi, barna ce mai manufa ta siyasa.
Tun a lokacin yakin neman zabe ne dai Donald Trump ya yi alkawalin fitar da kasarsa daga cikin yarjejeniyar ta kare muhalli, kuma bayan cin zabe ya cika alkawalinsa.
A 2015 ne dai aka cimma yarjejeniyar Paris ta kare muhalli da kasashe 200 suka rattaba hannu akansa.An kuma fara aiki da ita ce a 2016.