Pars Today
Kasashen Nijar, Mali da Chadi sun sanya hannu kan wata yarjejeniya ta aiki tare a tsakaninsu a fagen lamurran da suka shafi shari'a a kokarin da kasashen suke yi na fada da matsaloli na tsaro da suke fuskanta.
Rundinar sojin Chadi ta tabbatar a hukumance da kashe sojojinta tara da kuma jikkatar wasu 20 a yayin wani hari da 'yan ta'addan boko haram suka kai masu a garin Kaiga.
A jiya alhamis ne wata kotun birnin Njamina ta yanke hukuncin zaman kurkuku na watanni 6 ga Nadjo Kaina da Betrand Solloh.
Kotun musamman ta kungiyar Tarayyar Afirka ta tabbatar da hukuncin daurin rai-da-ran da aka yanke wa tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre bayan da aka same shi da aikata laifufukan yaki lokacin da ya ke kan karagar mulkin kasar Chadin.
Hukumar samar da abinci da kula da ayyukan noma ta Majalisar Dinkin Duniya "FAO" ta yi gargadi kan yiyuwar bullar masifar karancin abinci a yankin tafkin Chadi sakamakon rikicin kungiyar Boko Haram.
Yan adawa a kasar Chadi sun bukaci gudanar da zabukan 'yan Majalisun Dokokin Kasar a lokacin da doka ta tsayar.
Tawagar kwamitin tsaro na MDD dake ran gadi a yankin tafkin Chadi ta samu ganawa da hukumomin Nijar dana Chadi .
Rahotanni daga Chadi na cewa wasu mutane da ba'a san ko suwa ne ba ko kuma manufarsu sun sace wani dan gwagwarmaya a kasar.
Shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno ya sanar da yin gagarumin garanbawul wa majalisar ministocinsa inda ya shigo da sabbin fuskoki cikin sabuwar majalisar ministocin.
Shugaban kasar Chadi Idriss Derby ya sake sanar da jinkirta lokacin zaben ‘yan majalisar kasar wanda ya kamata a gudanar da shi tun a bariya, saboda matsalar rashin kudi da ake fuskanta.