An Sace Wani Dan Gwagwarmaya A Chadi
Rahotanni daga Chadi na cewa wasu mutane da ba'a san ko suwa ne ba ko kuma manufarsu sun sace wani dan gwagwarmaya a kasar.
Dan gwagwarmayan mai suna Daniel Ngadjadoum wanda kuma shi ne editan jaridar ''le Visionnaire'' an sace shi ne jiya Lahadi bayan fitowarsa daga coci.
A kasar Chadi dai 'yan jarida na fuskantar barazana a cikin aikinsu.
Da yake maida martani dangane da lamarin, shugaban kungiyar 'yan jarida na kasar ta Chadi, Belangar Larme, ya yi Allah wadai da sace dan jaridar.
A kasar ta Chadi 'yan jarida da 'yan gwagwarmaya basa da 'yancin gudanar da aikinsu cikin walwala inda a koda yaushe suke shan farauta daga jami'an hukumar leken asiri ta kasar.
A wasu lokutan kuma iyalen mutanen da ake tsarewa basa samun labari ko ganawa da 'yan uwansu.
Har kawo yanzu dai akwai iyalan wadanan mutanen biyar da cafke a yankin Mondu aka kuma tusa keyarsa a N'Jamena babban birnin kasar basu da labarin 'yan uwansu.