Gwamnatin Chadi Ta Sanar Da Sake Dage Lokacin Zabe Saboda Matsalar Kudi
(last modified Sat, 04 Feb 2017 05:36:08 GMT )
Feb 04, 2017 05:36 UTC
  • Gwamnatin Chadi Ta Sanar Da Sake Dage Lokacin Zabe Saboda Matsalar Kudi

Shugaban kasar Chadi Idriss Derby ya sake sanar da jinkirta lokacin zaben ‘yan majalisar kasar wanda ya kamata a gudanar da shi tun a bariya, saboda matsalar rashin kudi da ake fuskanta.

Shugaba Derby ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai jim kadan bayan dawowarsa daga taron shugabannin kasashen Afirka da aka gudanar a kasar Habasha inda ya ce gwamnatin ba za ta iya gudanar da zaben ba ne saboda ba ta da kudi yana mai shan alwashin gudanar da zaben a duk lokacin da aka sami damar yi.

Har ila yau shugaba Derby ya kirayi 'yan adawan kasar da su amince da tattaunawa don magance matsalar kasar kamar yadda kuma ya jinjina wa sojojin kasar saboda nasarar da suke samu a kan Boko Haram.

Tun a watan Mayun shekara ta 2015 ne ya kamata a gudanar da zaben sai dai shugaban ya ce babu kudin da za a gudanar.