Shugaban Kasar Chadi Yayi Garanbawul Wa Majalisar Ministocinsa
(last modified Mon, 06 Feb 2017 17:31:21 GMT )
Feb 06, 2017 17:31 UTC
  • Shugaban Kasar Chadi Yayi Garanbawul Wa Majalisar Ministocinsa

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno ya sanar da yin gagarumin garanbawul wa majalisar ministocinsa inda ya shigo da sabbin fuskoki cikin sabuwar majalisar ministocin.

Kafar watsa labaran Africanews ta bayyana cewar shugaba Idris Deby ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya sanar da cewa an nada Hissein Brahim Taha, wanda shi ne jakadar kasar Chadin a kasar Faransa a matsayin ministan harkokin waje wanda zai maye gurbin Moussa Faki Mahmat wanda ya zama shugaban kungiyar Tarayyar Afirka.

Har ila yau daga cikin sabbin fuskoki a sabuwar gwamnatin ta Chadi har da Christine Georges Diguibaye, wanda jami'i ne  kungiyar Tarayyar Afirka da ke Addis Ababa, a matsayin ministan kudi sai kuma Ahmat Mahamat Hassan a matsayin ministan shari'a.

An jima ana rade-radin gudanar da garanbawul din musamman bayan zaban da aka yi wa Moussa Faki Mahmat, tsohon ministan waje a matsayin sabon shugaban kungiyar Tarayyar Afirka da kuma korar ministan kudi da tsare tsare Mbogo Ngabo Selil da aka yi.