Tawagar MDD Ta Gana Da Hukumomin Nijar Da Chadi
Mar 05, 2017 11:19 UTC
Tawagar kwamitin tsaro na MDD dake ran gadi a yankin tafkin Chadi ta samu ganawa da hukumomin Nijar dana Chadi .
A kasar Chadi wakilan sun samu ganawa da rundinar hadin gwiwa ta kasashen yankin dake yaki da Boko Haram.
Rundinar ta ce ta kashe 'yan boko Haram 828 da kuma cafke wasu 615 daga watan Janairu na wannan shekara zuwa yanzu.
A Jamhuriya Nijar kuwu tawagar ta gana da Shugaban kasar Issufu Mahamadu wanda ya yi musu bayyani kan halin da kasar ke ciki akan yaki da kungiyar ta Boko Haram.
Dama kafin hakan tawagar ta MDD ta ziyarci yabkin arewa mai nisa na kasar Kamaru.
Tags