Pars Today
Gwamnatin hadin kan kasa ta kasar Libya ta ba da sanarwar cewa ba za ta halarci taron tattalin arziki na kasashen Larabawa wanda za'a gudanar a kasar Lebanon ba.
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya sake zargin tsohon shugaban kasar Libiya, mirigayi Muammar Ghaddafi da zame ummul-aba'isin tabarbarewar al'amuran tsaro a kasashen yammacin Afrika dana tsakiya da dama.
Manzon Musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Kasar Libya ne ya bayyana cewa za a gudanar da zaben shugaban kasa a kasar
Kasar Libiya ta fitar sammaci 37 na kame wasu 'yan tawayen kasashen Chadi da kuma Sudan dama wasu 'yan Libiya, da ake zargi da hannu a hare haren da aka kai kan wasu cibiyoyin man fetur da kuma wani sansanin soji.
Kakakin sojan kasar Libya ya sanar a jiya Talata cewa; Sojojin kasar sun yi nasarar kwato da mutane 21 da 'yan ta'adda su ka yi garkuwa da su
Rahotanni daga Libiya na cewa mutum uku ne suka rasa rayukansu, kana wasu goma na daban suka raunana bayan wani hari da aka kai a ma'aikatar harkokin wajen kasar dake birnin Tripoli.
Dan tsohon shugaban kasar Libya Saiful Islam ya nemi kariya da kuma goyon bayan shugaban kasar Rasha don sake komawa kan kujerar shugabancin kasar Libya.
Wata kungiyar bada agaji mai zaman kanta ta kasar Espania ta bada sanarwan cewa ta ceto bakin haure kimani 300 daga halaka a tekin Medeterenian.
Jami'i mai kula da tsaro da sulhu a kungiyar Tarayyar Afrika ya bayyana cewa rikicin kasar Libya yayi mummunan tasiri a dukkan kasashen Afrika.
Kungiyar Alkalai ta kasar Libya ta bada sanarwan cewa wasu yan bindiga sun kai hari kan wata kotun majestry a birnin Bangazi a ranar Alhamis da nufin hana kotun aiki da kuma kwace fursinonin da aka gurfanar a kotun da karfi