An Ceci Bakin Haure Kimani 300 Daga Halaka A Tekun Medeteranian
Wata kungiyar bada agaji mai zaman kanta ta kasar Espania ta bada sanarwan cewa ta ceto bakin haure kimani 300 daga halaka a tekin Medeterenian.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa AFP ya nakalto kungiyar "Pro-activa Open Arms" ta kasar Espania tana fadar haka, ta kuma kara da cewa daga cikin wadanda aka ceto akwai yara da mata da dama.
A rahoton da hukumar yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta bayar dangane da kwararar bakin haure zuwa kasashen turai, ta ce hanyoyin da bakin hauren suke bi zuwa kasashen na Turai, wadanda kuma suka fi hatsari, sune ta zuwa hanyar Malta da kuma ta Italia.
Labarin ya kara da cewa a cikin shekara ta 2018 da muke ciki, bakin haure kimani 1,300 suka halaka a kokarinsu na tsallakawa zuwa wadannan wurare.
kwararan bakin hauren yana ci gaba duk tare da tsauraran matakai wadanda gwamnatocin kasashen na Turai suke dauka kan bakin hauren.