Saiful Islam Ya Nemi Goyon Bayan Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin
Dan tsohon shugaban kasar Libya Saiful Islam ya nemi kariya da kuma goyon bayan shugaban kasar Rasha don sake komawa kan kujerar shugabancin kasar Libya.
Kamfanin dillancin labaran Spotnic na kasar Rasha ya bayyana cewa Saiful Islam ya bayyana wannan bukatar ne a wata wasika da ya rubutawa shugaban kasar ta Rasha Vladimir Putin inda ya bukacin goyon bayan shugaban don ya sami damar shiga cikin harkokin siyasa a kasar ta Libya.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Mikhail Bogdanov a maida martani ga wannan wasikar ya bayyana cewa gwamnatin kasar Rasha tana da ra'yin cewa a bar dukkan bamgarori na kasar Libya su shiga cikin lamuran siyasar kasar.
Kafin haka ma wani mai magana da yawan shi Saiful Isalam ya gana da Bogdanov a birnin Mosco inda ya gabatar masa da bukatar dan tsohon shugaban kasar.
Masu adawa da Saiful Islam dai suna ganin duk wani kokarin da zai yi na dawowa cikin harkokin siyasar kasar Libya kamar mahaifinsa ne ya dawo kan kujerar shugabancin kasar, abinda ba za su amince ba.