Tarayyar Afrika Ta Damu Da Tashe-Tashen Hankula Na Kasar Libya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i34485-tarayyar_afrika_ta_damu_da_tashe_tashen_hankula_na_kasar_libya
Jami'i mai kula da tsaro da sulhu a kungiyar Tarayyar Afrika ya bayyana cewa rikicin kasar Libya yayi mummunan tasiri a dukkan kasashen Afrika.
(last modified 2018-12-19T18:56:27+00:00 )
Dec 19, 2018 18:56 UTC
  • Tarayyar Afrika Ta Damu Da Tashe-Tashen Hankula Na Kasar Libya

Jami'i mai kula da tsaro da sulhu a kungiyar Tarayyar Afrika ya bayyana cewa rikicin kasar Libya yayi mummunan tasiri a dukkan kasashen Afrika.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Isma'ila Sharqi, jami'i mai kula da tsaro da kuma sulhu a kungiyar tarayyar Afrika yana fadar haka a yau Laraba a wani taron da ya halatta a kasar Algeriya.

Isma'il sharqi ya kara da cewa, kasashen Afrika sun sami ci gaba a bangaren tsaro a cikin yan shekarun da suka gabata, amma rikicin yankin Sahel da kuma na kasar Libya sun yi mummunan tasiri a dukkan kasashen nahiyar.

Jami'in ya kara da cewa, watakila rikicin da ke faruwa a yankin Sahel yana da nasaba da tabarbarewan harkokin tsaro a kasar Libya ne. Don haka, matsalar tsaro a kasar Libya ita ce babbar matsalar da ta addabi nahiyar Afrika gaba daya.