Libiya Ba Za Ta Halarci Taron Tattalin Arzikin Beyrut Ba
Gwamnatin hadin kan kasa ta kasar Libya ta ba da sanarwar cewa ba za ta halarci taron tattalin arziki na kasashen Larabawa wanda za'a gudanar a kasar Lebanon ba.
Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto majiyar gwamnatin kasar ta Libya tana fadar haka a jiya Litinin ta kuma kara da cewa bayan zanga-zangar kin jinin kasar da aka gudanar a birnin Beyrut babban birnin kasar ya zama dole ba zata iya halattar taron ba.
Bayan da Firai ministan rikon kwarya Sa'ad Alhariri ya gabbaya kasar ta Libya don halattan taron tattalin arziki na kasashen Larabawa a birnin Beyrut a ranar 20 ga wannan watan da muke ciki ne wasu yan siyasa a kasar ta Lebanon musamman magoya bayan kungiyar Amal ta yan shia suka gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da kasar ta Libya dangane da bacewar babban malamin na kuma shugaban kungiyar ta Amal wanda kuma ya kafata Imam Musa sadr a shekara ta 1978 bayan ziyarar da gwamnatin kasar ta lokacin ta bukace shi ya yi zuwa kasar, amma har yanzun kimani shekaru 40 kenan babu duriyarsa.