-
Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Ta Bada Umurnin Kama Tsohon Gwamnan Jihar
May 24, 2017 01:53Majalisar dokokin jihar Kebbi a tarayyar Nigeria ta bada umurnin kama tsohon gwamnan jihar Usman Sa'idu Dakingari, bayan da ta bashi lokaci zuwa jiya Talata na ya bayyana a gaban majalisar don amsa tambayoyi kan kontaragin gina tashan jiragen sama na jihar.
-
Jami'an Custom A Nigeria Sun Kwace Wasu Bindigogi Da Aka Shigo Da Su Kasar Ta Lagos
May 24, 2017 01:52Jami'an Custom a Nigeria sun sake kama wata Containa makare da bindigogi a tashar Jiragen ruwa ta Tin Can Islanda a birnin Lagosa, a jiya Talata.
-
Gwamnatin Jihar Kaduna Zata Rufe Wasu Manya Manyan Kamfanoni Saboda Rashin Biyan Haraji
May 20, 2017 13:42Ma'aikatar samarwa gwamnatin jihar kaduna kudaden shiga ta ce ta sami izinin kotu na rufe wasu manya manyan kamfanoni wadanda suke kaucewa biyar haraji a jihar.
-
An Hallaka Wasu 'Yan Kunar Bakin Wake Da ke Son Kai Harin Sashen Mata Na Jami'ar Maiduguri
May 19, 2017 13:23Rahotanni daga birnin Maiduguri na jihar Bornon Nijeriya sun bayyana cewar an hallaka wasu 'yan kunar bakin wake su uku a daidai lokacin da suke kokarin kai hari dakunan kwanan dalibai mata na jami'ar Maidugurin a daren jiya Alhamis.
-
Gwamnatin Najeriya Ta Yi Kira Ga Sogojin Ivory Coast Masu Bore Da Su Koma Barikokinsu
May 18, 2017 02:22Gwamnatin tarayyar Nigeria ta yi Allah wadai da boren da wasu tsirarun sojojin kasar Ivory coast suke yi, ta kuma yi kira gare su da su koma barikokinsu.
-
Mukaddashin Shugaban Najeriya Ya Ce Shi Ne Zai Sanya Hannu Kan Kasasfin Kudin 2017
May 18, 2017 02:13Mukaddashin shugaban kasar Nigeria Yemi Osinbajo Ya ce shi ne zai sanya hannu kan kasafin kudi na wannan shekara ta 2017 idan ya tabbatar da cewa an tsara shi yadda yakamata.
-
Sojojin Nigeriya Sun Kame Wani Babban Kwamandan Kungiyar Boko Haram
May 16, 2017 07:46Rundunar sojin Nigeriya ta sanar da kama daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram a jihar Yobe da ke shiyar arewa maso gabashin kasar.
-
Boko Haram Ta Kashe Wasu Manoma A Jihar Bornon Najeriya
May 15, 2017 14:43Wasu gungun 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun kashe wasu manoma shida a kauyen Amrawa da ke nisan kilomita 16 da garin Maiduguri fadar mulkin jihar Borno a shiyar arewa maso gabashin tarayyar Nigeriya.
-
Nijeriya : Ana Daukan Matakan kariya bayan Bullar Ebola A DRC
May 13, 2017 13:31Hukumar kula da tashoshin jiragen sama ta Nijeriya (FAAN) ta sanar da cewa ta dauki dukkanin matakan da suka dace wajen sanya ido kan dukkanin filayen jiragen saman kasar sakamakon bullar cutar nan ta Ebola a kasar Demokradiyyar Kongo.
-
Rundunar Sojin Nijeriya: Sabon Faifan Boko Haram Farfaganda Ce Kawai
May 13, 2017 13:28Rundunar sojin Nijeriya ta yi watsi da barazanar da kungiyar Boko Haram ta yi cikin wani sabon faifan bidiyon da ta fitar inda ta yi barazanar kai hare-hare cikin birnin tarayyar Nijeriya, inda ta ce faifan bidiyon farfaganda ce kawai da kungiyar ta saba yi, don haka kada 'yan kasar su damu da su.