Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Ta Bada Umurnin Kama Tsohon Gwamnan Jihar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20662-majalisar_dokokin_jihar_kebbi_ta_bada_umurnin_kama_tsohon_gwamnan_jihar
Majalisar dokokin jihar Kebbi a tarayyar Nigeria ta bada umurnin kama tsohon gwamnan jihar Usman Sa'idu Dakingari, bayan da ta bashi lokaci zuwa jiya Talata na ya bayyana a gaban majalisar don amsa tambayoyi kan kontaragin gina tashan jiragen sama na jihar.
(last modified 2018-08-22T07:00:09+00:00 )
May 24, 2017 01:53 UTC
  • Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Ta Bada Umurnin Kama Tsohon Gwamnan Jihar

Majalisar dokokin jihar Kebbi a tarayyar Nigeria ta bada umurnin kama tsohon gwamnan jihar Usman Sa'idu Dakingari, bayan da ta bashi lokaci zuwa jiya Talata na ya bayyana a gaban majalisar don amsa tambayoyi kan kontaragin gina tashan jiragen sama na jihar.

Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta bayyana cewa a zaman da majalisar ta yi a jiya Talata kakakin majalisar Alhaji Samaila Abdulmumini Kamba ya bayyanawa wakilan majalisar kan cewa tsohon gwamnan bai zo ba kamar yadda suka bukace shi. A nan ne Aminu Mohammad Bunza daga mazabar Bunza ya kawo batun majalisar ta bada umurnin a kama shi.

Aikin gina tashar jeragen sama na birnin Kibbe dai ya lashe kudade naira billion 18, a lokacin da Dakin gari yake gwamnan Jihar, amma yan majalisar suna ganin gwamnan ya kara naira billion 6.4 kan kudaden da ake bukata don gina tashar. Da wannan dalilin ne suka bukace shi da ya zo gaban komitin da aka kafa a majalisar don amsa tambayoyi.

A lokacinda Daily Trust ta tuntubi makusantan tsohon gwamnar sun bayyana mata cewa suna da labari kan matakin da majalisar jihar ta dauka a kan maigidansu kuma zasu maida martani nan ba da dadewa ba.