Boko Haram Ta Kashe Wasu Manoma A Jihar Bornon Najeriya
Wasu gungun 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun kashe wasu manoma shida a kauyen Amrawa da ke nisan kilomita 16 da garin Maiduguri fadar mulkin jihar Borno a shiyar arewa maso gabashin tarayyar Nigeriya.
Rahotonni sun bayyana cewa: Wasu gungun 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun farma wasu manoma da sara da adduna a kauyen Amrawa da ke kusa da garin Maiduguri fadar mulkin jihar Borno a ranar Asabar da ta gabata a daidai lokacin da manoman suke gudanar da sharar gonakinsu ganin damina ta fara kunno kai, inda suka kama manoma shida tare da kashe su ta hanyar yanka tamkar raguna.
Sauran manoman da suka tsere daga farmakin 'yan ta'addan na kungiyar Boko Haram sun dauki matakin sanar da al'ummar kauyen na Amrawa, inda 'yan banga suka bi sawun 'yan ta'addan, kuma suka tarar da su a kauyen Sojori da ke makobtaka da Amrawa, inda suka yi nasarar halaka 'yan ta'adda guda hudu, sauran kuma suka tsere.