Sojojin Nigeriya Sun Kame Wani Babban Kwamandan Kungiyar Boko Haram
Rundunar sojin Nigeriya ta sanar da kama daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram a jihar Yobe da ke shiyar arewa maso gabashin kasar.
Babban jami'in hudda da jama'a na rundunar sojin Nigeriya Brigadier Janar Sani Kukasheka Usman ya sanar da cewa: Rundunar sojin Nigeriya da hadin gwiwar 'yan banga sun samu nasarar kama daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram a jihar Yobe mai suna Abubakar Adamu da ake masa lakabi da "Pepper".
Sanarwar ta kara da cewa: Kwamandan kungiyar ta Boko Haram Abubakar Adamu dan shekaru 35 a duniya an samu nasarar damkeshi ne a ranar Lahadi 14 ga wannan wata na Mayu a kusa da gidan kurkukun garin Potiskum da ke jihar Yobe a shiyar arewa maso gabashin Nigeriya.
Har ila yau binciken farko-farko na nuni da cewa: Abubakar Adamu dan asalin kauyen Yerimara da ke karamar hukumar Potiskum ne a jihar ta Yobe, kuma yana da hannu a jarin hare-haren da mayakan kungiyar ta Boko Haram ke kai wa a shiyar arewa maso gabashin kasar ta Nigeriya.