Nijeriya : Ana Daukan Matakan kariya bayan Bullar Ebola A DRC
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20348-nijeriya_ana_daukan_matakan_kariya_bayan_bullar_ebola_a_drc
Hukumar kula da tashoshin jiragen sama ta Nijeriya (FAAN) ta sanar da cewa ta dauki dukkanin matakan da suka dace wajen sanya ido kan dukkanin filayen jiragen saman kasar sakamakon bullar cutar nan ta Ebola a kasar Demokradiyyar Kongo.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
May 13, 2017 13:31 UTC
  •  Nijeriya : Ana Daukan Matakan kariya bayan Bullar Ebola A DRC

Hukumar kula da tashoshin jiragen sama ta Nijeriya (FAAN) ta sanar da cewa ta dauki dukkanin matakan da suka dace wajen sanya ido kan dukkanin filayen jiragen saman kasar sakamakon bullar cutar nan ta Ebola a kasar Demokradiyyar Kongo.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN) ya jiyo Mukaddashin babban manajar hukumar ta FAAN Henrietta Yakubu tana cewa duk da cewa babu jirgin sama kai tsaye daga Kongon zuwa Nijeriya, amma dai hukumar ta dauki dukkanin matakai na rigakafi a dukkanin filayen jiragen sama wajen sanya ido da kuma gudanar da bincike, ta hanyar sanya na'uori na zamani da suke iya gano wannan cutar.

Jami'ar ta kara da cewa tuni gwamnati ta ba da umurnin daukan dukkanin matakan da suka dace na kara sanya ido a filayen jiragen saman.

A jiya Juma'a ne Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta sanar da sake bulla cutar Ebolan a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo tana mai cewa alal akalla mutum guda ya mutu sakamakon cutar lamarin da ya sake tada hankulan kasashen duniya dangane da wannan cuta.