-
Madagaska : Ravalomanana Ya Taya Rajaolina Murna Lashe Zabe
Jan 10, 2019 01:22Dan takara da ya sha kaye a zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Madagaska, ya yi na'am da kayan da ya sha a zaben, tare da taya zababen shugaban kasar, Andry Rajoelina, murna kan nasara da ya samu.
-
A ranar 15 Ga Wata, ICC Za Ta Bayyana Matsayinta Kan Bukatar Belin Laurent Gbagbo
Jan 10, 2019 00:26Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC), ta ce zatayi wani zama a ranar Talata 15 ga watan Janairun nan domin duba bukatar bada belin tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo, da kuma ministansa na matasa Charles Ble Goude, da take tsare da bisa zargin cin zarafin bil adama.
-
Dan Adawa Felix Tshisekedi, Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa A DR Congo
Jan 09, 2019 23:54Dan takaran adawa a jamhuriya Demokuradiyyar Congo, Félix Tshisekedi, ya kafa tarihi, inda ya lashe zaben shugaban kasar tun a zagayen farko.
-
Mohamed Salah Ya Sake Lashe Kyautar Gwarzon Kwallon Kafa Na Afrika
Jan 09, 2019 07:44Dan wasan kwallon kafa na kasar Masar Mohamed Salah ya sake lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafan nahiyar Afirka na shekarar 2018, dan wasa na farko da ya lashe wannan lambar yabo shekaru biyu a jere.
-
Sudan : Ana Zanga Zangar Goyan Bayan El-Bashir
Jan 09, 2019 06:54A Sudan daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga zangar nuna goyan baya ga shugaban kasar Omar Hassan El-Bashir, a Khartoum babban birnin kasar.
-
An Tabbatar Da Zabar Andry Rajoelina A Matsayin Shugaban Kasar Madagascar
Jan 09, 2019 03:52Babban kotun tsarin mulkin kasar Madagascar ce ta tabbatar da Andry Rajoelina a matsayin wanda ya yi galaba akan abokin hamayyarsa Marc Ravalomanana a zaben da aka gudanar a kasar
-
An Rusa Wata Kungiyar Mai Alaka Da Da'esh A Kasar Moroko
Jan 09, 2019 03:47Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Moroko ce ta sanar da rusa wata kungiya a arewacin kasar wacce take da alaka da kungiyar Da'esh
-
Zaman Lafiya Ya Dawo A Babban Birnin Kasar Gabon
Jan 09, 2019 03:40Bayan yunkurin juyin mulkin da wasu sojoji su ka yi a Gabon zaman lafiya ya sake dawowa
-
An Fara Sauraren Wadanda Sukayi Yunkurin Juyin Mulki A Gabon
Jan 08, 2019 14:13Rahotanni daga Gabon na cewa an fara sauraren wadanda sukayi wunkurin juyin mulki a kasar, a daidai lokacin da 'yan kasar ke son ayi musu karin bayyani kan hakikanin abunda ya faru.
-
CAF : Masar Za Ta Karbi Bakuncin Gasar 2019
Jan 08, 2019 12:55Hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF, ta mallaka wa kasar Masar, ragamar gudanar da gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika na 2019, bayan data kwace nauyin gudanar da gasar ga kasar Kamaru.