Zaman Lafiya Ya Dawo A Babban Birnin Kasar Gabon
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34731-zaman_lafiya_ya_dawo_a_babban_birnin_kasar_gabon
Bayan yunkurin juyin mulkin da wasu sojoji su ka yi a Gabon zaman lafiya ya sake dawowa
(last modified 2019-01-09T03:40:34+00:00 )
Jan 09, 2019 03:40 UTC
  • Zaman Lafiya Ya Dawo A Babban Birnin Kasar Gabon

Bayan yunkurin juyin mulkin da wasu sojoji su ka yi a Gabon zaman lafiya ya sake dawowa

Kamfanin dillancin labarun Faransa ne ya ba da labarin yunkurin juyin mulkin da wasu sojoji su ka so yi a ranar Litinin din da ta gabata, sai dai jami'an tsaron kasar sun murkushe shi

Sojojin sun fara da kwace iko da Radiyon kasar inda su ka yi sanarwar kafa majalisar tafiyar da harkokin mulkin kasar. 

Majiyar tsaron kasar ta Gabon ta ce an kama tare da kashe wasu daga cikin wadanda su ka shirya juyin mulkin

Rahotannin da suke fitowa daga babban birnin kasar sun ce harkokin yau da kullum suna tafiya kamar yadda aka saba a cikin babban birnin kasar libreville

Kwanaki kadan gabanin juyin mulkin Amurka ta aike da sojojinta zuwa cikin kasar ta Gabon, abin da ya sa wasu majiyoyi ke zargin cewa tana da masaniyar abin da zai faru

Shugaban kasar Ali Bongo yana kwance a asibiti a kasar Moroko inda yake yin jiyya rashin lafiyar da yake fama da ita