An Fara Sauraren Wadanda Sukayi Yunkurin Juyin Mulki A Gabon
Rahotanni daga Gabon na cewa an fara sauraren wadanda sukayi wunkurin juyin mulki a kasar, a daidai lokacin da 'yan kasar ke son ayi musu karin bayyani kan hakikanin abunda ya faru.
Wata majiya ta tabbatarwa da kamfanin dilancin labaren AFP cewa, kawo yanzu babu bayyani akan ko wadanda sukayi yunkurin juyin mulkin sun samu umarni daga manyan sojoji ko kuma 'yan siyasa.
Kawo yanzu bayanai sun nuna cewa al'amura sun daidaita a Libreville babban birnin kasar, inda kuma aka maido da hanyoyin sadarwa na intanet, da kuma na kafofin sada zumunta, kuma tuni makarantu da kasuwanni da ma'aikatun gwamnati suka bude.
Bayanai sun nuna cewa an cafke takwas daga cikin wadanda sukayi yunkurin juyin mulki a yayinda aka kashe guda biyu, saidai babu labari akan adadin fararen hula da aka cafke a lokacin da sukayi kokarin yin zanga zangar goyan bayan yujin mulkin.
Mahukuntan kasar sun ce, daga cikin wadanda aka cafke har da jagoransu laftana Ondo Obiang Kelly, wanda ya karanta sanarwa juyin mulkin a gidan rediyo da talabijin na kasar.