Jan 08, 2019 16:25 UTC
  • CAF : Masar Za Ta Karbi Bakuncin Gasar 2019

Hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF, ta mallaka wa kasar Masar, ragamar gudanar da gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika na 2019, bayan data kwace nauyin gudanar da gasar ga kasar Kamaru.

Hukumar ta CAF ta sanar da hakan ne yau Talata a yayin wani taron kwamitin kolinta a birnin Dakar na kasar Senegal.

Dama dai kasashen Masar da AFrika ta Kudu ne suka bayyana sha'awarsu ta neman karbar bakuncin gasar ta 2019, bayan da aka kwace shirya gasar ga kasar Kamaru saboda matsalar tsaro da kuma tsaiko wajen aiwatar da wasu ayyuka dake da nasaba da filayen kwallo.

A nasu bangare hukumomin kasar ta Masar sun sha alwashin gudanar da gasar cikin cikaken tsaro. 

Wannan dai ba shi ne karo na farko da Masar zata karbi bakuncin gasar ba, don sau hudu take karbar gasar, wanda kuma ta karshe ita ce wacceta gudanar a shekara 2006, amma wannan kuma ita ce ta farko tun bayan juyin juya hali na 2011 da y7a kawo karshen mulkin shugaba Hosni Moubarak, wanda ya jefa kasar cikin matsalar tsaro.

Masar dai nada manyan filayen kwallon kafa, da kuma filayen jirgin sama na kasa da kasa guda biyu, da kuma manyan Otel otel wanda za'ayi amfani dasu a gasar ta bana da za'a farawa a cikin watan Yuni.

 

Tags