An Tabbatar Da Zabar Andry Rajoelina A Matsayin Shugaban Kasar Madagascar
Babban kotun tsarin mulkin kasar Madagascar ce ta tabbatar da Andry Rajoelina a matsayin wanda ya yi galaba akan abokin hamayyarsa Marc Ravalomanana a zaben da aka gudanar a kasar
Babban alkalin kotun tsarin mulkin kasar ta Madagascar Eric Rakotoarisoa ne ya sanar da cewa; Rajoelina wanda ya sami kaso 55.66 na jumillar kuri'un da aka kada, shi ne wanda ya lashe zaben shugaban kasar
Gabanin gudanar da zaben 'yan takarar shugabancin kasar biyu sun yi alkawalin karbar sakamakon zaben na 19 ga watan Disamba, sai dai bayan gudanar da zaben, Marc Ravalomanan ya shigar da kara a gababn kotun tsarin mulki ta kasar yana neman da a rusa sakamakon zaben
Cibiyar zaben dan hamayyar Ravalomanana sun yi zargin cewa an keta ka'idojin zaben har 200 tare da gabatar da bayanai ga kotun tsarin mulkin kasar.
Sai dai masu sa ido na kasa da kasa da su ka hada da tarayyar turai sun kore cewa an sami magudi a cikin zaben
A ranar 19 ga watan Disamba ne aka yi zaben shugaban kasa zagaye na biyu a kasar ta Madagascar