Madagaska : Ravalomanana Ya Taya Rajaolina Murna Lashe Zabe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34747-madagaska_ravalomanana_ya_taya_rajaolina_murna_lashe_zabe
Dan takara da ya sha kaye a zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Madagaska, ya yi na'am da kayan da ya sha a zaben, tare da taya zababen shugaban kasar, Andry Rajoelina, murna kan nasara da ya samu.
(last modified 2019-01-10T01:22:49+00:00 )
Jan 10, 2019 01:22 UTC
  • Madagaska : Ravalomanana Ya Taya Rajaolina Murna Lashe Zabe

Dan takara da ya sha kaye a zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Madagaska, ya yi na'am da kayan da ya sha a zaben, tare da taya zababen shugaban kasar, Andry Rajoelina, murna kan nasara da ya samu.

A wani gajeren sakon bidiyo mai dauke da jawabinsa, Mista Ravalomanana, ya ce, ''an zabi Andry Rajoelina a matsayin shugaban kasa, a don haka ina mai taya sa murna''

Bayanin na tsohon shugaban kasar ta Madagaska kana dan takara da ya sha kaye a zaben shugaban kasar a zagaye na biyu, na zuwa ne bayan da kotun tsarin mulkin kasar ta tabbatar da zabin da akayi wa Mista Andry Rajoelina wanda shi ma tsohon shugaban kasar ne.

Wannan dai ya kawo karshen fargabar da ake da ita na zaben zai kawo tashin hankali a wannan kasar ta Madagaska.

A shekarenn jiya ne kotun tsarin mulki a Madagaska, ta amince da nazara da dan takara Andry Rajoelina ya samu a zaben shugaban kasar zagaye na biyu.

Kotun ta kuma ayyana tsohon shugaban kasar Andry Rajoelina, mai shekaru 44 a matsayin zababen shugaban kasar, tare da yin watsi da dukkan korafen korafen da dan takaran da ya sha kaye Marc Ravalomanana ya gabatar mata, bayan zaben na ranar 19 ga watan Disamba da ya gabata.

A ranar 19 ga watan Janairun nan ne ake sa ran rantsar dashi a matsayin sabon shugaban kasar.

Mista Rajoelina ya dai lashe zaben ne da kashi 55,65% na yawan kuri'un da aka kada, a yayinda babban aboklin hammayarsa Marc Ravalomanana ya samu kashi 44,34%, sakamakon da dan takaran Ravalomanana ya yi watsi dashi yana mai zargin tafka magudi a lokacin.