Sakamakon Zaben Nijar
Shugaba Mai Ci Muhammadu Yusuf Ne Akan Gaba
Kamfanin Dillacin Labarun Faransa ya nakalto hukumar zaben kasar Nijar na cewa; shugaban kasa mai ci, Muhammadu Yusufu ne ke kan gaba da kaso 47%.1.
Sanarwar da hukumar zaben "Ceni' ta fitar a dazu wacce ta kunshi kaso 86% na jumillar kuri'un da aka kada, ta bayyana cewa; Muhammadu Issoufou ya sami kaso 48.41, sai kuma Hama Amadou da ya ke bi masa da kaso 17.79 %.
Shi dai Hama, yana tsare a gidan kaso saboda zarginsa da ake yi da cinikin jarirai daga kasashen makwabta, sai dai ya musanta zargin.
Za a sake zuwa zagaye na biyu na zaben shugaban kasar a tsakanin Muhammadu Issoufu da kuma Hama Amadou anan gaba.
Mutane 15 ne su ka tsaya takarar shugabancin kasar.
Bayan ga zaben shugaban kasa, al'ummar kasar sun kuma kada kuri'ar zaben 'yan majalisar dokoki.
Kungiyar Tarayyar Afirka wacce ta aike da masu sa-ido 40 ta bayyana gamsuwarta akan yadda zaben ya gudana cikin lumana, duk da cewa an sami jinkirin kai kayan aiki a wasu mazabun.