Hatsarin Jirgin Sama Ya Kashe Wasu Sojojin Kamaru Guda Hudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i16923-hatsarin_jirgin_sama_ya_kashe_wasu_sojojin_kamaru_guda_hudu
Rahotanni daga kasar Kamaru sun bayyana cewar wasu sojojin kasar Kamaru guda 4 sun rasa rayukansu sakamakon faduwar jirgin saman da yake dauke da su a yankin Bogo da ke arewacin kasar Kamarun.
(last modified 2018-08-22T06:59:34+00:00 )
Jan 23, 2017 07:40 UTC
  • Hatsarin Jirgin Sama Ya Kashe Wasu Sojojin Kamaru Guda Hudu

Rahotanni daga kasar Kamaru sun bayyana cewar wasu sojojin kasar Kamaru guda 4 sun rasa rayukansu sakamakon faduwar jirgin saman da yake dauke da su a yankin Bogo da ke arewacin kasar Kamarun.

Kafafen watsa labaran kasar Kamarun sun ce lamarin ya faru ne a jiya Lahadi a lokacin da jirgin saman mai saukar ungulu yayi hatsari dauke da hafsoshin sojin a kan hanyarsu ta zuwa wani aiki a ci gaba da fada da 'yan kungiyar Boko Haram da sojojin kasar suke yi.

Wata majiyar soja ta ce daga cikin wadanda suka rasu din har da Janar Jacob Kodji kwamandan runduna ta 4 da ke yaki da kungiyar ‘Yan Boko Haram.

Kasar Kamaru din dai tana daga cikin kasashen Yammacin Afirka da suke fuskantar matsalar kungiyar ta Boko Haram inda suke ci gaba da kai hare-haren ta'addanci a kasar.