Kamaru : An Cafke Masu Alaka Da Boko Haram 106
Rahotanni daga Kamaru na cewa mutane 106 ne ake tsare da bisa zarginsu da alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram.
Galibin mutanen an cafke su ne a garin Mozogo dake yankin arewa mai nisa na Jamhuriya ta Kamaru kamar yadda kanfanin dilancin APA ya rawaito.
Wasu bayanai da jaridar « L’œil du Sahel » da ake bugawa a kasar ta Kamaru ta rawaito sun ce an cafke mutanen ne a cikin watan Fabarirun daya gabata.
A yayin samamen da rundinar hadin hadin gwiwa ta kasashen yankin dake yaki da kungiyar boko haram ta kai a yankin ne aka cafke mutanen a cewar rahotannin.
Gwamnatin Kamaru dai ta tanadi doka ta musamman dangane da ayyukan ta'addanci, wace take kaiwa har ga hukuncin kisa kan duk wani mahaluki da aka samu da laifin kai hare-hare ko kuma bayar da hadin kai ga kungiyar Boko Haram.