Kotu Ta Yanke Wa 'Yan Sanda Biyu Hukuncin Kisa A Najeriya
Mar 09, 2017 13:24 UTC
Wata kotu a birnin Abuja fadar mulkin Najeriya, ta yanke wa wasu jami'an 'yan sanda biyu hukuncin kisa bayan samunsu da laifin kisan kai na ganganci a kan wasu 'yan kasuwa.
Babban alkali mai shari'a a kotun Ishaq Bello ya ce 'yan sandan biyu suna daga cikin wadanda suka aikata lifin kisan kai a kan wasu 'yan kasuwa 6 a cikin shekara ta 2005 a birnin na Abuja.
Bayanin ya kotun ya kara da cewa, 'yan sandan sun aikata kisan ne a matsayin 'yan fashi da makami, kuma yanzu haka akwai wasu da ake zargi suna da hannu a cikin lamarin da suka hada har da shugaban ofishin 'yan sanda na unguwar Apo da ke cikin birnin Abuja, wadanda suka tsere tun bayan faruwar lamarin.
Tags