Hare-Haren Ta'addanci Ne Musabbabin Rashin Zaman Lafiya A Yammacin Afrika
Shugaban kasar Liberia Malama Ellen Johnson Sirleaf ta bayyana cewa hare haren ta'addanci a wasu kasashen yankin yammacin Afrika su ne suke samar da rashin zaman lafiya a yankin
Majiyar muryar JMI daga birnin Monrovia babban birnin kasar Liberia, inda shuwagabannin kasashen kungiyar raya tattalin arziki na yammacin Afrika (ECOWAS) suke gudanar da taro, a jiya Lahadi ya nakalto Malama Ellen Johnson Sirleaf tana fadar haka. Ta kuma kara jaddada bukatar bukatar a samar da hnayar fita daga wadannan matsaloli.
Malaman Ellen Johnson Sirleaf dai ita ce shugaban kungiyar ta ECOWAS sannan ta yaba da yadda mayakan kungiyar suka sami nasarar dawo da zaman lafiya a kasarta Liberia.
A cikin watan Yulin shekara ta 2016 ne Ellen Johnson Sirleaf ta karbi ragamar shugabancin ECOWAS a taron kungiyar a birnin Dakar na kasar Senegal.