An Zarki 'Yan Kasar Habasha 10 Da Aiyukan Ta'addanci
Wata Kotu a kasar Habasha ta zarki 'yan kasar 10 da laifin aikata ta'addanci tsakanin shekarar 2015 zuwa 2017.
Kamfanin dillancin Labaran Xin huwa na kasar China ya habarta cewa 'yan kasar Ethiopiar 10 an zarke su ne da laifin ingiza Al'umma da kuma tayar da hankali a garin Gondar dake arewacin Adis Ababa fadar milkin kasar
Har ila yau an zarki mutanan goma da tayar da riciki a wani taron Addini na mabiyan Addinin Kirista na Orthodox a garin Gondar tare kuma da kokari wajen ingiza Al'ummar kasar wajen tayar da bore a sassa daban daban na kasar.
Idan ba a banta dai , kasar Eritrea ta kasance wani yankin na kasar Ethiopia, amma bayan bore da mutanan yankin suka yi daga shekarar 1952 zuwa shekarar 1993, an gudanar da zaben jin ra'ayin Al'umma na ballewa daga yankin, inda Al'ummar yankin suka zabi ballewa daga kasar ta Ethiopia.