Tununsiya Na Nemen Kujerar Shugaban Majalisar Kungiyar Tarayyar Afirka
'Yan siyasar kasar Tununsiya sun bukaci kasar da ta nemi kujerar shugaban majalisar kungiyar AU domin kalubalantar kokarin haramtacciyar kasar Isr'aila na samun wuri a majalisar.
Kafar watsa labaran Al-arabie Jadidi ya habarta cewa duk da irin sabanin siyasa da tattalin arzikin dake akwai a tsakanin 'yan majalisar dokokin kasar Tunusiya, dukkanin 'yan majalisun sun nuna goyon bayansu ga dan majalisar munji Arrahwi wakilin kasar Tunusiya a Majalisar kungiyar tarayyar Afirka da ya nemi kujerar shugabancin Majalisar domin kalubalantar hukumomin HKI na kokarin da suke yi na samun wuri a kungiyar.
Ma'aikatar harakokin wajen Tunusiya ta hanyar Narjas Duraidi jakadan kasar a kasar Afirka ta kudu ta farfagandar sharan fage na halartar zaben majalisar kungiyar tarayyar Afirkan mai zuwa.
A nasa bangare shugaban kasar Tunusiya Beji Caid Essebsi ya goyi bayan takarar Rahwi a Majalisar ta AU duk kuwa da sabanin siyasar dake a tsakaninsu.
A cewar Faisal Tabaini wani dan majalisar kungiyar AU, kasar Tunusiya ta kalubalanci bukatar hukumomin HKI na kasancewarta a matsayin manba na masu sanya ido a majalisar kungiyar ta AU.
Majalisar ta AU nada manbobi 230 da suka fito daga kasashen Afirka 46.