An bayyana Ranar Zaben Majalisar Dokoki A Kasar Gabon
(last modified Thu, 22 Feb 2018 11:54:25 GMT )
Feb 22, 2018 11:54 UTC
  • An bayyana Ranar Zaben Majalisar Dokoki A Kasar Gabon

Gwamnatin kasar Gabon ta bayyana ranar da za'a gudanar da zaben majalisar dokokin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar China ya nakalto kakakin gwamnatin kasar kuma ministan sadarwa Alain Claude Bilie yana fadar haka a yau Alhamis.

Ministan ya kara da cewa za'a gudanar da zaben ne a ranar 28 ga watan Afrili mai zuwa kamar yadda babban kotun kasar ta amince. Labarin ya kara da cewa za'a yi takaran cike kujeru 140 ne a sabon majalisar dokokin kasar wato tare da karin kujeru 20 a kan yawan yan majalisa a gwamnatin da ta shude.

Banda haka kakakin gwamnatin ya ce za'a kafa wata sabuwar hukumar zabe wacce zata maye gurbin ta yanzun kafin lokacin zaben.