'Yan Gudun Hijrar Kwango 5 Sun Mutu A Ruwanda
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28539-'yan_gudun_hijrar_kwango_5_sun_mutu_a_ruwanda
'Yan sandar kasar Ruwanda sun sanar da mutuwar 'yan gudun hijrar kasar jamhoriyar Kwango 5 a yayin zanga-zangar kin jinin hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya FAO
(last modified 2018-08-22T07:01:28+00:00 )
Feb 24, 2018 15:32 UTC
  • 'Yan Gudun Hijrar Kwango 5 Sun Mutu A Ruwanda

'Yan sandar kasar Ruwanda sun sanar da mutuwar 'yan gudun hijrar kasar jamhoriyar Kwango 5 a yayin zanga-zangar kin jinin hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya FAO

Kakakin 'yan sandar kasar Ruwanda Theos Badege ya sanar a wannan Asabar cewa 'yan gudun hijrar kasar Demokariyar Kwango dake samun mafaka a sansanin 'yan gudun hijra na MDD dake cikin kasar ne suke gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadinsu kan yanayin mu'amalar da hukumar samar da abinci ta MDD wato FAO ke yi da su, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutun biyar , yayin da wasu 20 na daban suka samu rauni.

Kakakin 'yan sanda ya ce daga cikin wadanda suka jikkata har da jami'an tsaro bakwai.

Zanga-zangar ta 'yan gudun hijra na zuwa ne bisa kudirin da hukumar samar da abinci ta MDD wato FAO ta dauka na rage kashi 25% na taimakon dake bayarwa ga sansanin 'yan gudun hijrar Kiziba dake yammacin kasar Uganda, lamarin da ya tayar da jijiyoyin wadanda aka tsugunar a cikin wannan sansani.

An fara zanga-zangar ne tun a ranar talalar da ta gabata har zuwa ranar jiya juma'a.