Guinea Conakry: Zanga-zangar Kin Amincewa Da Sakamakon Zabe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28595-guinea_conakry_zanga_zangar_kin_amincewa_da_sakamakon_zabe
Mazauna babban birnin kasar ta Guinea Conakry sun shiga zaman dirshen da kuma gudanar da Zanga-zanga domin kim amincewa da sakamakon zabe
(last modified 2018-08-22T07:01:29+00:00 )
Feb 26, 2018 15:35 UTC
  • Guinea Conakry: Zanga-zangar Kin Amincewa Da Sakamakon Zabe

Mazauna babban birnin kasar ta Guinea Conakry sun shiga zaman dirshen da kuma gudanar da Zanga-zanga domin kim amincewa da sakamakon zabe

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ce; Dubban mutane ne a birnin Conakry suka shiga Zanga-zangar nuna kin amincewa da sakamakon zaben  biranen da aka gabatar.

Masu Zanga-zangar sun rika kona tayoyi a manyan tituna tare da hana kai da komowar mutane.

Kungiyoyin ma'aikata da kuma 'yan hamayyar siyasa suna zargin cewa an yi magudi a cikin zaben da aka gudanar a ranar 4 ga watan Febrairu.

Jam'iyyun adawa sun yi barazanar fadada Zanga-zangar tasu zuwa dukkanin bangarorin kasar.