Rikicin Kabilanci Ya Lakume Rayukan Mutane 22 A Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28613-rikicin_kabilanci_ya_lakume_rayukan_mutane_22_a_congo
Rikicin kabilanci a arewacin Democradiyyar Congo ya lakume rayukan mutane akalla 22
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Feb 27, 2018 04:39 UTC
  • Rikicin Kabilanci Ya Lakume Rayukan Mutane 22 A Congo

Rikicin kabilanci a arewacin Democradiyyar Congo ya lakume rayukan mutane akalla 22

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa an yi rigimar ne a tsakanin kabilun hutu da Nonad a ranakun lahadi da litinin da suka gabata kuma an kashe fararen hula 15 sannan an kashe yan bindiga 7.

Labarin ya kara da cewa mayakan kabilar Hutu ne suka farwa yan kabilar Nonad a garuruwansu na Buwalondo da kuma Kolusi. 

Yankunan tsakiya da gabas da kuma arewacin kasar Congo suna fama da tashe tashen hankula fiye da shekaru 20 da suka gabata. Sojojin kasar da kuma na majalisar dinkin duniya sun kasa tabbatar da zaman lafiya a wadannan yankun, wanda yasa rikicin yake kara fadi a ko wace shekara