Rwanda: Za A Rufe Wuraren Ibada Fiye Da 700 Daga Gobe Alhamis
Feb 28, 2018 15:22 UTC
Gwamnatin kasar ta Rwanda ta dauki matakin rufe majami'u fiye da 700 saboda babu tsaro da kuma tsafta a cikinsu
Wani jami'in gwamnatin kasar ta Rwanda Anastas Shika ya sanar da cewa; Wuraren Ibadar da za a fara rufewa daga gobe alhamis sun kai 714, daga cikinsu da akwai masallaci daya.
Wuraren ibadar dai suna a cikin babban birnin kasar ne da kuma sauran garuruwan kasar.
Shika ya kara da cewa; Wasu daga cikin wuraren ibada suna a wuraren da babu kyakkyawan yanayi a ciki ta fuskar lafiya ko kuma ta fuskar tsaro.
Daga cikin dalilan rufe wuraren ibadar da akwai sauti mai karfi da suke fitarwa wanda yake damun mutane, kamar yadda jami'in gwamnatin ya bayyana.