Rikicin Kabilanci Ya Ci Rayukan Mutane Da Dama A Kasar Kwango
Majiyar tsaron jamhoriyar Demokaradiyar Kwango ta sanar da hallakar mutane da dama sanadiyar rikicin kabilanci a jahar Ituri dake arewa maso gabashin kasar
Kamfanin dillancin labaran Xin huwa ya nakalto majiyar tsaron jamhoriyar demokaradiyar kwango na cewa akalla mutane 40 ne suka hallaka sanadiyar ricikin kabilancin da ya auku a daren jiya alhamis tsakanin kabilar Hema da lendu a wani kauye na jahar Ituri dake arewa maso gabashin kasar.
Majiyar ta ce tuni dai gwamnati ta kira taron gaggauwa domin tattaunawa kan halin da jahar Ituri ke ciki, kuma an tura karin jami'an tsaro yankin domin kwantar da tarzoma.
Watani biyu da suka gabata, kabilun Hema da Lendu sun yi irin wannan fada da ya lashe rayukan sama da mutane dari a yankin.
Sama da shekaru 20 kenan, da yankunan tsakiya da arewa maso gabashin kasar ta Kwango ke fuskantar matsalar tsaro.
Kasawar jami'an tsaron kasar da dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD wajen kawo karshen kungiyoyin 'yan tawaye a kasar ta Kwango ya kara fadada rashin tsaro da tashin hankali a kasar.