Majalisar Dinkin Duniya Ta Nuna Damuwa Akan Rikicin Kabilancin Kasar Congo
Dakarun tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Congo Sun yi tir da fadan kabilancin da ya faru a cikin kasar.
Kamfanin dillancin labarun faransa ya ambato dakarun da ake kira MONUSCO na yin tir da fadan da ya faru tsakanin kabilun Hema da Lendu a yankin Ituri da ke arewa maso gabashin kasar.
Dakarun na Majalisar Dinkin Duniya sun kuma sanar da shirinsu na tuntubar dukkanin bangarorin al'ummar kasar da dukkanin bangarorin da suka dace domin hana afkuwar fadan a nan gaba.
Majiyar tsaron jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta ce; Adadin wadanda suka rasa raukan nasu sanadiyyar fadan sun kai mutane 40 mafi yawancinsu mata da kananan yara.
A cikin watanni biyu na bayan nan kabilun Hema da Lendu sun yi fadace-fadacen da su ka ci rayuka fiye da 100.