Bankin Duniya Ya Yi Gargadi Akan Tattalin Arzikin Kasar Moroko
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28995-bankin_duniya_ya_yi_gargadi_akan_tattalin_arzikin_kasar_moroko
Kamfanin dillancin labarun Xinhua ya ce; Wajibi ne ga kasar ta Moroko da ta kawar da matsalaolin da suke gabata, idan tana son kare ci gaban da ta samu a tattalin arzikinta
(last modified 2018-08-22T07:01:33+00:00 )
Mar 12, 2018 05:48 UTC
  • Bankin Duniya Ya Yi Gargadi Akan Tattalin Arzikin Kasar Moroko

Kamfanin dillancin labarun Xinhua ya ce; Wajibi ne ga kasar ta Moroko da ta kawar da matsalaolin da suke gabata, idan tana son kare ci gaban da ta samu a tattalin arzikinta

Bankin duniyar ya ci gaba da cewa; Babbar matsalar da tattalin arzikin kasar ta Moroko yake fuskanta ita ce rashin tsayayyen tanadi akan samar da aikin yi a tsakanin samarin kasar.

Sai dai rahoton ya yabawa tattalin arzikin Moroko akan jawo zuba hannun jari da samar da kayan aiki na zamani da kuma ba da horo ga ma'aikata.

Sai dai duk da haka da akwai bukatar akawar da matsalolin da tattalin arzikin yake fuskanta domin kare ci gaban da ya samu.